12 Satumba 2021 - 13:13
Shugaban Hukumar IAEA, Na Ziyara A Tehran

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Rafael Grossi, ya fara wata ziyara a birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ziyarar dai na da manufar samar da wata yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin Tehran kan wasu batutuwa masu tsarkakiya.

Yayin ziyarar tasa Mista Grossi, zai gana da sabon shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami.

Wannan dai ita ce ziyara irinta ta farko da shugaban hukumar ta IAEA, ya kawo a Iran, tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin kasar ta Ebrahim Ra’isi.

Nan gaba ne ake sa ran bangarorin biyu zasu fitar da wata sanarwa.

A kwanan dai hukumar ta IAEA, ta fitar da wani rahoto inda take nuna damuwa game da rashin samun hadin kai daga Iran kan binciken data sabayi lokaci zuwa lokaci.

Iran dai ta takaita sanya ido na hukumar da kuma daina baiwa hukumar hotunan bidiyon da kyamarori ke dauka a cibiyoyin nkiliyarta.

Amurka da kasashen turai dai sun bukaci Iran data gaggauta komawa tattaunawar Vienna ta farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015, saidai Iran ta ce tana bukatar akalla wata uku domin nada sabbin mambobin da zasu wakilce ta a tattaunawar.

342/